Ingantaccan Tsarin Abinci (Hausa)

Healthy Eating Plate Hausa

Ingantaccen tsarin abinci, wanda kwararru kan kimiyyar abinci na sashen lafiyar al’umma da ke jami’ar Harvard tare da masu tace dab’in kiwon lafiya na Harvard suka kirkiro, wani jagora ne na samar da ingantacce kuma lafiyyen abinci mai gina jiki – a faranti ne ko kwanon da aka iya dauka a tafi da shi.  A saka kwafi  a jikin firinji a matsayin matashiyar samar da abinci mai gina jiki.

  • Mafi yawan abincin ka ya zama ganyayyaki ne da ‘ya’yan itace – ½ na kwanon ka:

Ka lura da launi da kuma nau’I kuma a kiyaye cewa dangogin dankali basa daga cikin  ganyayyaki a tsarin ingantaccen abinci saboda rashin kyan tasirin su a cikin jini.

  • Zabi zallar hatsi – ¼ na kwanon ka:

Zallar hatsi marar sirki – kamar alkama dawa jar shinkafa da sauran dangin su da kuma abincin da aka samar daga garesu kamar taliyar alkama na da saukin illa ga sugan dake cikin jini da kuma sinadarin da ke sarrafa shi wanda ake kira (insulin) fiye da farin biredi ko farar shinkafa da sauran nau’I na hatsin da aka surfe shi aka kuma sarrafa shi.

  • Abinci mai gina jiki – ¼ na kwanon ka:

Kifi, kaji, wake da irin su gyada da gurjiya  duka hanyoyi ne da ake samun lafiyayye kuma ingantaccen abinci mai gina jiki – ana gauraya su a cikin salak kuma suna haduwa yadda ya kamata da sauran ganyayyaki a cikin abinci. A takaita cin naman dabbobi da ake kira jan nama kuma a kaucewa naman da aka riga aka sarrafa shi kamar malkadadden naman gwangwani da ake kira a turance “bacon” da kuma “sausage”.

  • Tsaftataccen man tsirrai – daidai misali:

Amfani da lafiyayyen man tsirrai kamar man zaitun, man soya ko na gero da  ire-iren su (canola, sunflower, peanuts) a kuma kaucewa man da aka surka shi wanda ke dauke da maiko marar amfani. Kada kuma a manta cewa maiko dan ba wai bashi da wata illa ba ne.

  • Ka sha ruwa, kofi ko shayi:

Barin shan zaki, takaita shan madara da sauran ababen da aka yi su da nonon shanu ya kasance sau daya ko biyu a rana, haka nan lemon jus kada ya wuce kofi daya a rana.

  • Kasance cikin kuzari:

Wannan zanen mai launin ja da ke gudu bisa tabarmar ingantaccen tsarin abinci matashiya ce cewa motsa jiki shima yana da muhimmanci wajen rage nauyi.

Muhimmin sakon ingantaccen tsarin abinci shine mayar da hankali kan ingancin abinci

  • Nau’in sinadarin sa kuzari (carbohydrate) da ke cikin abincin shine ya fi muhimmanci fiye da yawan sa domin wadansu sinadaran kuzarin kamar ganyayyaki (ban da irin su dankali) ‘yayan itace, Hatsi da wake – su kan fi wasu inganci.
  • Haka kuma ingantaccen tsarin abinci na shawartar jama’a su kauracewa shayeshayen kayan zaki, kasancewar su wata babbar hanyar tara maiko a jiki – kuma gasu da karancin amfani a jiki.
  • Ingantaccen tsarin abinci na karfafawa jama’a gwiwa su yi amfani da sahihin mai, kuma bas u iyakance adadin maikon da mutum zai samu a kullum daga lafiyayyen kitse ba.

Translation assistance provided by Dr. Sally N. Adebamowo

Terms of Use

The contents of this website are for educational purposes and are not intended to offer personal medical advice. You should seek the advice of your physician or other qualified health provider with any questions you may have regarding a medical condition. Never disregard professional medical advice or delay in seeking it because of something you have read on this website. The Nutrition Source does not recommend or endorse any products.